Golden E-SPORT
RAHOTO
Isak ya matsu ya bar Newcastle, Man Utd na fatan daidaitawa da Lammens

Ɗan wasan Sweden Alexander Isak mai shekara 25, ya faɗa wa Newcastle yana son rabuwa da ita zuwa Liverpool duk da shiga tsakani da shugaban ƙungiyar, Yasir Al-Rumayyan da kuma tattaunawa da ɗaya daga cikin masu ƙungiyar, Jamie Reuben. (Telegraph - subscription required, external)
Manchester United ta cimma yarjejeniya da ɗan wasan Real Betis mai shekara 25, Antony wanda za ta ba shi damar ya je zaman aro kafin daga bisani a yanke hukuncin zaman dindindin. (Telegraph - subscription required, external)
Manchester United na kuma fatan nasarar saye mai tsaron raga, Senne Lammens daga Royal Antwerp kafin a rufe kasuwar cinikin 'yan wasa. (Telegraph - subscription required, external)
Real Madrid da Atletico Madrid na bibbiyar ɗan wasan Manchester United da Ingila, Kobbie Mainoo mai shekara 20. (Mail, external)
🚨⚠️ An ci mutuncin Kylian Mbappé da Vini Jr.
An ci mutuncin Kylian Mbappé da Vini Jr. ta hanyar nuna wariyar launin fata jiya da daddare a Oviedo.
Masu kallo biyu suna yin sautin 'birrai' a kansu,”* in ji rahoton Diario AS
Abin takaici ne ƙwarai. Wulakanci ne wannan.
Jackson zai je Bayern Munich, Hojlund na nazari kan Napoli

Chelsea ta amince da yarjejeniyar ba da aron ɗan wasanta na Senegal, mai shekara 24, Nicolas Jackson ga Bayern Munich. (Bild - in German)
Ɗan wasan tsakiya a Ingila, Kobbie Mainoo mai shekara 20, na nazarin barin Manchester United nan gaba kaɗan. (Talksport)
Palace ta gabatar da tayin fam miliyan 15 kan ɗan wasan Manchester City Manuel Akanji, mai shekara 30. (Sun)
Ɗan wasan gaba a Manchester United da Denmark Rasmus Hojlund mai shekara 22, zai samu karin albashi idan ya amince ya koma Napoli. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Tottenham na son Savinho, Ƙungiyoyi na rububin Rodrygo

Ɗan wasa Savinho daga Manchester City ya kasance wanda Tottenham ke so ido rufe, yayinda kocinsu Thomas Frank ya dage don ganin lallai ya saye matashin mai shekara 21 daga Brazil, musamman ganin sun yi rashin nasarar daidaitawa kan Eberechi Eze mai shekara 27, da ya je Arsenal. (Independent)
ta gabatar da tayi kan ɗan wasan Manchester City, kuma ta ce za ta biya fam miliyan 60.7 don ganin ta mallake Savinho, wanda ke burin komawa Landan. (Talksport)
A kokarin ganin ta ɗauko sabbin 'yanwasa biyu, Tottenham ta amince da yarjejeniyar fam miliyan 43 kan ɗan wasan Como da Argentina, Nico Paz mai shekara 20, amma ƙungiyarsa ta Italiya na neman fam miiyan 60.(Sky Sports Italia - in Italian)
Manchester City da Arsenal da Liverpool na son ɗan wasan Real Madrid da Brazil, Rodrygo mai shekara 24, amma ƙungiyarsa ta Sifaniya ba ta karɓi tayi daga kowa ba tukkunan. (Marca - in Spanish)

Ta yaya Arsenal ta yi nasarar sayen Eze?
Sayen Eberechi Eze ya canza tunanin magoya bayan Arsenal baki ɗaya.
Gunners ta yi namijin ƙoƙari a wannan lokacin a kasuwar cinikayyar ƴan ƙwallo, inda ta saya ƴan'wasa shida kan fam miliyan 190 tun kan fara kakar tamaula ta bana.
Daga cikin ƴan'wasan har da Viktor Gyokeres kan fam miliyan 64 da Martin Zubimendi kan fam miliyan 60, sai dai sayen Eze da ta yi, wanda hakan ya sa magoya baya na ganin ita ce kan gaba a cefane mai amfani.
Wani babban al'amari shi ne yadda Arsenmal ta sha gaban abokiyar hamayyarta Tottenham Hotspur, wadda tun farko ta ƙulla yarjejeniyar shiga ciniki da Crystal Palace da Eze sa'o'i kafin Gunners ta shiga zawarcin ɗan wasan.